Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
An bukaci gwamnatin Jihar Plateau da ta fitar da takardar rahoto (white paper) kan hare-haren baya-bayan nan da kisan-kisan da suka faru a wasu al’ummomi a jihar.
An yi wannan kira ne a ranar Lahadi daga Kwamitin Zaman Lafiya na Jihar Plateau (Plateau State Executive Peace Roundtable) karkashin shirin Delimi Prosper Project, a cikin wata sanarwa da suka fitar bayan kammala taronsu da aka gudanar a Jos.
A cikin makonnin baya-bayan nan, wasu al’ummomi a Jihar Plateau sun fuskanci karuwar hare-hare, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da lalata dukiyoyi.
Sanarwar wadda Nanmak Bali ya sanya wa hannu ta bayyana cewa taron ya tattauna ra’ayoyin matasa da kuma abubuwan da suka fuskanta a rayuwa dangane da hanyoyin da ba na amfani da karfi ba (non-kinetic) da kuma hanyoyin rigakafi wajen magance rikice-rikicen da suka shafi albarkatun kasa.
Daga karshe suka yanke shawarar cewa gwamnati ta fitar da takardar rahoto kan hare-haren tare da aiwatar da shawarwarin da ke cikinta.
Karanta:INTERNATIONAL WOMEN’S DAY 2026: Plateau Govt Reaffirms Commitment to Women Empowerment
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati ciki har da Sakataren Gwamnatin Jihar Plateau, Samuel Jatau, da Babbar Darakta Janar ta Hukumar Gina Zaman Lafiya ta Plateau, Julie Sanda.
Har ila yau, mahalarta taron sun ba da shawarar kafa tsaron al’umma (community policing), wayar da kan jama’a, da kuma tattaunawa domin amfani da damar da kafafen dijital ke bayarwa wajen samar da alheri.
Sauran shawarwarin sun hada da tuntubar hukumomin da ke sa ido kan dokoki domin magance karya ka’idoji, da kuma samar da gidajen tarihi da wuraren nuni (galleries da museums) domin ba da labaran al’umma ta hanyar amfani da dandamalin dijital.
Recent:Bwala: Why govt spokespersons need communication training — PDP chieftain.
