Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Bassey Ewah, ta kai ziyara zuwa wasu yankunan da ake fuskantar matsalar tsaro a cikin biranen Jos da Bukuru, domin rage tashin hankali da kuma tabbatar wa mazauna yankunan cewa ana kokarin tabbatar da zaman lafiya.
Ziyarar wadda aka gudanar a yau ta hada jami’an tsaro daga rundunar soji da sauran hukumomin tsaro, inda suka kai duba zuwa wurare da dama da suka hada da Mararaban Jama’a, Kasuwar Terminus Jos, Farin Gada, yankin Bukuru da kasuwar shanun Bukuru, Dadin Kowa, da kuma Abattoir.
Yayin da yake jawabi ga shugabannin Kasuwar Shanun Bukuru, CP Bassey Ewah ya tabbatar musu da cewa jami’an tsaro na aiki tukuru domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Ya kuma bukace su da su ci gaba da harkokinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro ba, tare da rokon su rika sanar da jami’an tsaro duk wani abu da suka gani na zargi.
Karanta:Atiku ya yi Allah-wadai da kashe-kashe da sace fiye da mutane 100 a wani ƙauyen Borno.
A nasa bangaren, Kwamandan Rundunar Sojin Sama ta Najeriya a NAF 551 Jos, Air Commodore F.O. Bassey, ya bayyana cewa sun fito ne domin tallafawa ‘yan sanda wadanda ke da alhakin tsaron cikin gida. Ya jaddada cewa duk wanda aka samu yana haddasa rikici ko tayar da fitina ba za a bar shi ba.
Rundunar ‘yan sandan ta ce wannan zagayen duba tsaro na nuna kudurin ta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin Jihar Filato.
Haka kuma rundunar ta bukaci al’umma su rika kai rahoton duk wani abu na zargi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma su kira lambobin gaggawa na rundunar.
Recent:Iyalan El-Rufai sun buƙaci a sake shi ba tare da ɓata lokaci ba
