Rundunar juyin juya halin Iran IRGC ta yi gargaɗin cewa za ta kai hari kan matatun mai guda biyar a ƙasashen Saudiya da Qatar, da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) “a cikin ‘yan sa’o’i masu zuwa.”
Gargadin ya ce waɗannan “wurare sun zama abin hari kai tsaye.”
Karanta:Jam’iyyar LP ta sanya 23 ga watan Mayu domin zaben fidda gwani na shugaban ƙasa
Iran ta fitar da wannan gargaɗin ne awa ɗaya bayan rahotannin da ke cewa Isra’ila ta kai hari ta sama a wani kamfanin samar da iskar Gas da ke filin haƙar iskar gas na South Pars.
Filin na South Pars dai shi ne filin haƙo iskar gas mafi girma a duniya, wanda Qatar da Iran ke amfani da shi tare.
Recent:Sibil Difens ta jibge jami’anta 700 don tabbatar da tsaro a Gombe domin bukukuwan sallar.
