Wata kotu a ƙasar Amurka ta bayar da umarni ga tsohon Shugaban ƙasa Donald Trump da ya maido da sama da ma’aikata 1,000 na gidan rediyon Voice of America (VOA) da aka dakatar daga aiki.
Karanta:Gwamnan Filato Ya kori Wasu Mukarraban Siyasa, Ya Dakatar da Shugaban Hukuma
Alkalin kotun, Royce Lamberth, ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, inda ya bayyana cewa matakin rage yawan ma’aikatan da aka dauka a karkashin jagorancin Kari Lake bai bi ka’ida ba. Saboda haka, kotun ta umarci a mayar da ma’aikatan bakin aiki kafin ranar 23 ga watan Maris.
Haka kuma, kotun ta bukaci US Agency for Global Media da ta gabatar da tsari mai kyau na yadda za a ci gaba da yada shirye-shiryen VOA zuwa sassa daban-daban na duniya kamar yadda aka saba.
Voice of America, wadda aka kafa bayan Yakin Duniya na Biyu, na daga cikin manyan kafafen yada labarai na gwamnatin Amurka, tana kuma watsa shirye-shirye cikin harsuna kusan 49 ga miliyoyin masu sauraro a duniya.
Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan ‘yancin kafafen yada labarai da kuma rawar da gwamnati ke takawa wajen tafiyar da su.
Recent:Gwamnan Filato Ya kori Wasu Mukarraban Siyasa, Ya Dakatar da Shugaban Hukuma
