An sanar da Mojtaba Khamenei a matsayin sabon Jagoran Addinin ƙasar Iran bayan rasuwar mahaifinsa, Ali Khamenei, wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana jagorantar ƙasar.
Sabon jagoran, Mojtaba Khamenei, an haife shi a shekarar 1969 a garin Mashhad na ƙasar Iran. Malamin addini ne da ya yi karatu a makarantar malamai ta Qom, kuma ya dade yana da tasiri a harkokin siyasa da tsaro a ƙasar duk da cewa bai riƙe wani babban mukamin gwamnati a fili ba.
Rahotanni sun nuna cewa Mojtaba yana da kusanci da manyan jami’an tsaro da rundunar Revolutionary Guard, lamarin da ya sa ake kallonsa tun da dadewa a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da za su iya gaje mahaifinsa.
Karanta:Wane ne sabon sufetan ƴansandan Najeriya Tunji Disu?
Ana sa ran sabon jagoran zai ci gaba da tafiyar da manufofin siyasa da tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran kamar yadda mahaifinsa ya shimfiɗa.
