Amnesty International ta yi Allah-wadai da tsare Sani Waspapping ba bisa ka’ida ba da aka ce jami’an Department of State Services (DSS) sun yi.
An kama Sani Waspapping ne a Kaduna ranar Juma’a, kuma har yanzu yana tsare ba tare da an ba shi damar ganin iyalansa ko lauyoyinsa ba. Rahotanni sun nuna cewa ana zargin kamun nasa yana da alaƙa da sakonnin da ya wallafa a kafafen sada zumunta game da yaƙin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.
Karanta:Kotu Ta Ci Tarar Gwamnatin Kano Miliyan 1 A Shari’arta Da Tsofaffin Kwamishinoni
A halin yanzu, Sani Waspapping shi ne mutum na biyu da DSS ta tsare dangane da halin da ake ciki na yaƙin Gabas ta Tsakiya.
Amnesty International ta bukaci hukumomin Najeriya su bi dokokin ƙasa a kowane lokaci, har da batun Sani Waspapping. Kungiyar ta ce dole ne a ba shi damar ganin iyalansa da lauyoyinsa cikin gaggawa, ko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu — idan kuma ba haka ba, a sake shi daga tsare nan take.
