By Mustapha Abdullahi Abubakar
Bayan yin shawarwari masu zurfi da shugabannin jami’an tsaro, Shugaban Ƙaramar Hukumar Mangu Hon.Emmanuel Bala Mwolpun, ya saka dokar hana fita a cikin garin Mangu, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Afrilu, 2026, har sai an sanar da wani lokaci na daban.
An tsara lokutan dokar hana fitar daga ƙarfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe kowace rana.
An ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a cikin garin.
Gwamnatin Ƙaramar Hukumar tana kira ga dukkan mazauna yankin da su bi wannan doka. An shawarci jama’a da su zauna a cikin gidajensu a lokacin dokar hana fita, tare da ba jami’an tsaro haɗin kai yayin da suke bakin aiki.
Shugaban Ƙaramar Hukumar mangun ya kuma roƙi mazauna yankin da su gudanar da harkokinsu cikin lumana tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi ga hukumomin da suka dace.
An ɗora wannan dokar hana fita ne domin kare lafiyar jama’a da tabbatar da tsaro.
Recent:Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya
