Daga Mustapha Abdullahi
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta musanta wata sanarwa da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ta sanya ranar 26 ga Maris a matsayin wa’adin da jami’an gwamnati masu son tsayawa takara za su yi murabus.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Juma’a, ta bayyana cewa bayanin da ke cikin sanarwar karya ne kuma ba daga hukumar ya fito ba.
Hukumar ta bukaci jama’a, kafafen yada labarai da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da su yi watsi da sanarwar gaba ɗaya, tana mai jaddada cewa ba ta fitar da irin wannan sanarwa ba.
Karanta:An kori mutane 22 a Jigawa sakamakon badakalar ciyarwar a watan Ramadan.
INEC ta kuma shawarci ‘yan Najeriya da su rika dogaro da hanyoyin sadarwa na hukuma na hukumar, kamar shafinta na intanet, shafukan sada zumunta da aka tabbatar, da kuma takardun sanarwar manema labarai domin samun sahihan bayanai.
Hakazalika, hukumar ta gargadi jama’a da su guji yada bayanan zabe marasa tabbaci da ka iya rikitar da jama’a, tana mai cewa za ta ci gaba da samar da sahihan bayanai cikin gaskiya da lokaci.
Recent:Gwamnan Katsina ya yaba da karin girman mukamin Masari
