Daga Mustapha Abdullahi
A sabon tsarin farashi da matatar ta fitar a ranar 10 ga Maris, 2026, an rage farashin fetur a wajen lodin kaya (gantry) da ₦100, inda farashin ya sauka zuwa ₦1,075 kan kowace lita, daga tsohon farashin ₦1,175 kan kowace lita.
Matatar ta kuma bayyana cewa sabon farashin PMS domin jigilar da ake yi ta teku yanzu zai kasance ₦1,050 kan kowace lita, wanda ya haɗa da ƙaramin gyara saboda kuɗin jigilar ruwa.
Hakazalika, farashin Automotive Gas Oil (dizal) an rage shi zuwa ₦1,430 kan kowace lita a wajen lodin kaya (gantry).
Karata :Just In: Dangote Refinery Lowers Petrol Price by ₦100 to ₦1,075 Per Litre, Diesel Now ₦1,430.
Wannan na nufin an rage ₦190 daga tsohon farashin ₦1,620 kan kowace lita.
Matatar ta kuma bayyana cewa farashin da aka ambata a wajen lodin kaya bai haɗa da kuɗaɗen hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority ba.
Recent:From Evidence to Action: Bauchi Strengthens Maternal Nutrition Through MMS Scale-Up
