Daga mustpha Abdullahi Abubakar
Hukumar kiwon Lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi ta ƙaddamar da fara Rigakafin cutar Zazzabin Cizon Sauro a faɗin Jihar.

Da yake jawabi a lokacin fara Rigakafin, Shugaban Hukumar Dr Rilwanu Mohammed ya ce sun horas da jami’ai 4000 da zasu yi allurar riga-kafin.
Karanta:Hare-haren Borno: Za mu kawo ƙarshen ta’addanci da ƙarfin soja inji Shettima.
Dr Rilwanu Mohammed wanda ya samu wakilcin Daraktan dakile yaɗuwar cututtuka a Hukumar Dr Adamu Muhammad ya ce Rigakafin za fara yin ta ne a watanni 5 na farkon rayuwar Jariri, in da Rigakafi na biyu da na uku za a yi wa yaro ne bayan mako huɗu huɗu.

A jawabinsa wakilin Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya a wajen taron Dr Yarima Kuci ya ce a Najeriya ana samun masu kamuwa da ciwon zazzaɓin cizon sauro miliyan 260 duk shekara, in da cutar take ajalin mutane dubu ɗari shida da goma (610,000) a shekara.

Bincike ya gano cewa Jihar Bauchi tafi kowacce jiha a yankin Arewa maso Gabas yawan masu kamuwa cutar zazzaɓin cizon sauro.
