Daga Auwal Gsm Multimedia
An gudanar da gasar wasan Snooker domin ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kiristoci a birnin Jos, a ranar Asabar 25 ga Afrilu, 2026.

Gasar wadda ta samu halartar sama da mutane 40 daga addinai daban-daban, Alhaji Sadiq Nalele ne ya ɗauki nauyin shirya ta domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’umma.

An gudanar da wasan ne a babban filin wasan Snooker na E3 da ke kan titin Bauchi Road a Jos, inda mahalarta suka nuna farin ciki da nishaɗi yayin gudanar da gasar.
Karanta:CHAMPS, Partners Intensify Campaign Against Home Delivery in Bauchi
A ƙarshen wasan, mutane biyu ne suka kai matakin ƙarshe, inda Mr. Key ya zama zakara a matsayi na farko, yayin da abokin karawarsa Shata ya zo na biyu.

Da yake jawabi bayan kammala gasar, Alhaji Sadiq Nalele ya bayyana cewa an shirya wannan wasa ne musamman domin ƙarfafa haɗin kan al’umma da tabbatar da zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kiristoci.

Mai rahoto na Zenith Media ya rawaito cewa an gudanar da taron cikin annashuwa, tare da halartar jami’an tsaro daban-daban da suka haɗa da ‘yan sanda, DSS, NDLEA, sojoji, Civil Defence, da kuma Hunters.

An rufe taron da ɗaukar hotuna na tunawa tare da bayar da kyaututtuka (awards) ga duk waɗanda suka halarci gasar da kuma shugabannin jami’an tsaron da suka samu halarta.
Recent:UNICEF, GAC Support Bauchi Govt With 45 Motorcycles To Boost Maternal, Child Healthcare
