Daga Mustapha Abdullahi
Jam’iyyar ADC ta zargi jam’iyya mai mulki, APC, da ƙoƙarin amfani da hukumar zaɓe ta INEC domin haddasa rikici a cikin jam’iyyar, biyo bayan shigar tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, cikin ADC.
A wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar 31 ga Maris, 2026, ya ce gwamnatin tarayya ƙarƙashin APC na matsa lamba ga shugaban INEC, Joash Ojo Amupitan, domin ya tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar.
ADC ta ce shigar Kwankwaso cikin jam’iyyar ya tayar da hankali a APC, lamarin da ya sa ake ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa tare da hana manyan ‘yan siyasa sauya sheƙa zuwa ADC.
Jam’iyyar ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga wata wasiƙa da wasu manyan lauyoyi suka aika a ranar 28 ga Maris, suna neman INEC ta soke wasu muhimman matakai na jam’iyyar tare da sauya shugabancinta kafin kotu ta yanke hukunci na ƙarshe.
ADC ta ce wannan mataki na ƙoƙarin fassara hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ne ta wata hanya da ba ta dace ba, musamman dangane da batun “status quo ante bellum”, alhali shari’ar na gaban kotu.
Karanta:CURFEW A PLATEAU: AN DAMKE SOJAN GONA DA WASU 6
Haka kuma, jam’iyyar ta zargi cewa wasiƙar ta yi barazanar kama shugaban INEC idan bai bi buƙatun cikin kwanaki bakwai ba, abin da ta ce wani yunkuri ne na tilasta wa hukumar ta ɗauki ɓangare.
ADC ta jaddada cewa mutumin da ake magana a kai ba tsohon shugaban jam’iyya ba ne, kuma ba ɗan jam’iyyar bane a halin yanzu, domin ya yi murabus tare da wasu mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa kafin daga bisani a kore shi.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa waɗannan matakai na nuna fargaba da damuwa da ke cikin APC sakamakon karuwar karɓuwar ADC a faɗin ƙasar.
Recent:Kwankwasiyya ta soki Tinubu kan ciyo bashin dala biliyan 6
