Daga Mustapha Abdullahi
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, a yau Talata zai yanki katin zama ɗan jam’iyyar ADC a jihar Kano.
Gawuna ya fice daga jam’iyyar APC bayan ya ajiye mukaminsa na shugabancin bankin lamuni na ƙasa (FMBN).
karanta:POLICE PARADE OPERATIONAL SUCCESS, ANNOUNCE NATIONAL POLICE DAY 2026 ACTIVITIES IN PLATEAU
Wata sanarwa da aka fitar a daren jiya Litinin ta ce Gawuna zai yanki katin zama ɗan jam’iyyar ADC a yau Talata a mazaɓarsa ta Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nassarawa.
Sanarwar ta ce za a haɗu a kofar gidan Kwankwaso na Miller Road sannan a dunguma zuwa mazaɓar ta Gawuna domin yankar katin da misalin karfe 11 na safe.
