Daga Mustapha Abdullahi
An gurfanar da wani ma’aikacin hukumar kula da masu yiwa ƙasa hidima mai shekaru 43, Abbas Olalekan, a kotun majistare da ke Abeokuta bisa zargin haɗa baki da yunƙurin zubar da ciki ta hanyar ba da magunguna kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.
Mai gabatar da ƙara ya bayyana cewa wanda ake tuhuma ya yi hulɗa da wata ‘yar bautar ƙasa, inda ake zargin ya ɗirka mata ciki sannan ya ba ta magungunan da suka jawo mutuwarta.
Karanta:Bauchi APC Stakeholders Reject Moves to Alter Congress Outcome, Back Tinubu’s Re-election
Sai dai Olalekan ya musanta zargin.
Kotun ta bada belinsa kan naira 500,000 tare da sharudda, tare da umartar a tsare shi a gidan gyaran hali har sai ya cika sharuddan.
An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga Afrilu domin ci gaba da shari’a.
