MAIDUGURI
Bisa umarnin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya isa birnin Maiduguri domin duba halin da ake ciki bayan harin kunar bakin wake da ya faru.
A yayin ziyarar, IGP Disu ya kai ziyara asibiti inda ya gana da wadanda harin ya rutsa da su, yana mai jajanta musu tare da tabbatar da cewa jami’an tsaro za su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Haka kuma, ya ziyarci wuraren da harin ya faru domin tantance halin da ake ciki da kuma ba da umarnin ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin.
Karanta:Bauchi Youths Hold Bala Wunti Ramadan Cup to Promote Unity
Jar hular da IGP ɗin ke sanye da ita, ta musamman ce ta rundunar Police Counter Terrorism Unit (CTU), wadda ke nuna ƙudirin rundunar wajen yaƙar ‘yan ta’adda da duk wani nau’in barazana ga tsaron ƙasa.
Zenith Media News ta rawaito cewa wannan ziyara na daga cikin matakan gaggawa da gwamnati ke ɗauka domin daƙile hare-haren ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.
Recent:NEMA Distributes Relief Materials to Fire, Windstorm Victims in Niger
