An ci gaba da shari’ar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar Litinin 9 ga Maris 2026, inda shaida ta goma sha ɗaya (PW11), James Bem Igbakymeh, ta bayyana a gaban Mai shari’a Emeka Nwite na Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, yadda wani mutum mai suna Shehu Bello ya sayi wani gida da ke Wuse II, Abuja, kan kuɗi har ₦650 miliyan.
Hukumar EFCC na tuhumar Yahaya Bello da laifuka 19 da suka shafi zargin wanke kuɗaɗe har ₦80,246,470,088.88.
Shaidar, wanda lauya ne, ya bayyana wa kotu cewa a watan Oktoba 2021 wani abokin cinikinsa ya ba shi umarnin sayar da wani gida da ke Plot 1058, Cadastral Zone A08, Wuse II, Abuja.
Ya ce ya saka tutar talla a wurin domin jawo masu saye, sannan wani mutum mai suna Shehu Bello ya tuntube shi.
Ya ce bayan tattaunawa, sun amince da farashin ₦650 miliyan.
Shaidar ya ce an biya kuɗin ne ta asusun banki uku da abokin cinikinsa ya bayar:
- SFC Foods Limited – Polaris Bank
- JIT Agric Limited – Polaris Bank
- SFC Foods Limited – Heritage Bank
Ya ƙara da cewa an biya kuɗin ta hannun ’yan kasuwar canjin kuɗi (Bureau De Change) kafin a miƙa takardun gidan ga mai saye.
Daga baya, jami’an EFCC sun gayyace shi domin yin bayani a lokacin bincike. Ya ce ya je ofishin EFCC da ke Wuse II, Abuja, inda ya rubuta bayani kuma ya miƙa takardun da suka shafi cinikin.
Lokacin da aka nuna masa takardar tayin saye (Offer Letter) da kuma Deed of Assignment, ya tabbatar su ne takardun da aka yi amfani da su wajen cinikin.
Sai dai ya ce a cikin takardun, sunan wanda aka rubuta a matsayin mai karɓar gidan shi ne Ali Bello, ba Shehu Bello ba.
Da aka tambaye shi ko Ali Bello da Shehu Bello mutum ɗaya ne, sai ya amsa cewa a’a.
Ya bayyana cewa dukansu biyu ne suka riƙa zuwa tare yayin tattaunawar cinikin gidan.
A lokacin tambayoyin lauya na ɓangaren kariya, shaidar ya ce shi ba shi ne ya rubuta takardar Deed of Assignment ba, domin masu sayen gidan ne suka kawo masa ita.
Bayan ya gama bayar da shaidarsa, kotu ta sallame shi.
Karanta:Gwamna Mutfwang Ya Kaddamar da Rabon Kayan Karatu, Ya Buɗe Sabon Ginin Ofis na SUBEB a Jos
Shaida ta 12 ta EFCC
Daga nan EFCC ta gabatar da shaida ta 12, Jamilu Abdullahi, wanda ɗan kasuwar Bureau De Change ne.
Ya shaida wa kotu cewa yana da kamfanoni uku:
- Kunfayakun Global Limited
- E-Traders International Limited
- De-Remita International Limited
Ya ce a shekarar 2021 ya haɗu da wani mutum mai suna Abba Adaudu a Zenith Bank da ke Apo, Abuja, inda suka musayar lambobin waya bayan sun gano dukkansu suna harkar canjin kuɗi.
Ya ce daga baya Adaudu ya riƙa aika masa kuɗi domin ya mayar da su dala.
A cewarsa, an riƙa saka kuɗi a asusunsa a sassa-sassa na ₦10 miliyan.
Lokacin da aka nuna masa wasu kuɗaɗe da aka saka a Access Bank Lokoja a ranar 29 da 30 Disamba 2021 da suka kai ₦60 miliyan, sai ya ce shi ba shi ne ya saka kuɗin ba, sai dai Abba Adaudu.
Ya ƙara da cewa bai taɓa zuwa reshen Access Bank Lokoja ba a rayuwarsa.
Ya ce duk lokacin da aka saka kuɗi, yana canza su zuwa dala sannan ya ba Abba Adaudu.
Batun Tafiyar Yahaya Bello Ƙasashen Waje
A ƙarshen zaman kotu, lauyan EFCC Kemi Pinheiro, SAN ya roƙi kotu ta soke izinin da aka bai wa Yahaya Bello na tafiya ƙasashen waje, saboda wasu sabbin dalilai da suka shafi tsaro.
Sai dai lauyan Bello J.B. Daudu, SAN ya ƙi amincewa da wannan roƙo, yana mai cewa Bello yana kan belin kotu kuma har yanzu ana ɗaukarsa ba shi da laifi har sai an tabbatar.
Daga ƙarshe, Mai shari’a Emeka Nwite ya ɗage shari’ar zuwa:
- 22, 23 da 24 Afrilu 2026
- 6 da 7 Mayu 2026
domin ci gaba da sauraron shari’ar.
