By Mustapha Abdullahi Abubakar
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da tura jakadu da manyan kwamishinoni 65 zuwa kasashe daban-daban da kuma zuwa United Nations.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya ce an raba jakadu 31 wadanda ba ma’aikatan diflomasiyya na dindindin ba, da kuma 34 wadanda su ne ma’aikatan diflomasiyya na dindindin, zuwa wuraren aikinsu.
Tun a watan Disamba na shekarar 2025 ne Nigerian Senate ta tabbatar da dukkan mutane 65 bayan an yi musu tantancewa ta hannun kwamitin harkokin waje.
An kuma umarci Ministry of Foreign Affairs Nigeria da ta fara shirin horaswa (induction programme) ga wadannan jakadu, kafin su fara aiki bayan kasashen da za su je sun amince da nadinsu.
1) Sanata Grace Bent — Togo (Lomé)
2) Sanata Ita Enang — Afirka ta Kudu
3) Ikpeazu Victor — Spain
4) Nkechi Linda Ufochukwu — Isra’ila (Tel Aviv)
5) Mahmud Yakubu — Qatar
6) Paul Oga Adikwu — Vatican City
7) Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas — Philippines
8) Reno Omokri — Mexico
9) Engr. Abasi Braimah — Hungary (Budapest)
10 Mrs. Erelu Angela Adebayo — Portugal
11) Barr. Oluwayimika Ayotunwa — Japan (Tokyo)
12) Ifeanyi Lawrence Ugwuanyi — Greece (Athens)
13) Barr. Chioma Priscilla Ohakim — Poland (Warsaw)
14) Aminu Dalhatu — Birtaniya (Babban Kwamishina)
15) Lt. Gen. Abdulrahman Bello Dambazau — China (Beijing)
16) Hon. Tasiu Musa Maigari — Gambia
17) Olufemi Pedro — Australia
18) Barr. Muhammed Ubandoma Aliyu — Argentina
19) Lateef Kayode Are — Amurka
20) Amb. Joseph Sola Iji — Rasha
21) Sanata Jimoh Ibrahim — Wakilin
dindindin a Majalisar Dinkin Duniya
22) Femi Fani-Kayode — Jamus
23) Prof. Isaac Folorunso Adewole — Canada (Ottawa)
24) Fatima Florence Ajimobi — Austria
25) Mrs. Lola Akande — Sweden
26) Ayodele Oke — Faransa
27) Yakubu N. Gambo — Saudiyya
28) Sanata Prof. Nora Ladi Daduut — Koriya ta Kudu (Seoul)
29) Barr. Joe-Kyari Okocha — Ireland (Dublin)
30) Dr. Kulu Haruna Abubakar — Tunisia (Tunis)
31) Hon. Jerry Samuel Manwe — Trinidad da Tobago (Port of Spain)
Jakadu Masu Sana’ar Diflomasiyya (Career Ambassadors)
32) Nwabiola Ezenwa Chukwumeka — Côte d’Ivoire
33) Besto Maimuna Ibrahim — Nijar (Niamey)
34) Monica Okwuchukwu Enebechi — São Tomé da Príncipe
35) Mohammed Mahmud Lele — Aljeriya (Algiers)
36) Endoni Syndoph Paebi — Burkina Faso (Ouagadougou)
37) Ahmed Mohammed Monguno — Masar (Cairo)
38) Jane Adams — Jamaica (Kingston)
39) Clark-Omeru Alexandra — Zambia (Lusaka)
40) Chima Geoffrey Lioma David — Mali (Bamako)
40) Odumah Yvonne Ehinosen — Equatorial Guinea (Malabo)
41) Wasa Segun Ige — Lebanon (Beirut)
42) Ruben Abimbola Samuel — Italiya (Rome)
43) Onaga Ogechukwu Kingsley — Mozambique (Maputo)
45) Magaji Umar — DR Congo (Kinshasa)
46) Muhammad Saidu Dahiru — India (New Delhi)
47) Abdussalam Habu Zayyad — Senegal (Dakar)
48) Shehu Ilu Barde — Ghana (Accra)
49) Aminu Nasir — Ethiopia
50) Abubakar Musa — Chadi (N’Djamena)
51) Haidara Mohammed Idris — Netherlands (The Hague)
52) Bako Adamu Umar — Morocco (Rabat)
53) Sulu Gambari Olatunji Ahmed — Malaysia
54) Romata Mohammed Omobolanle — Tanzania
55) Shaga John Shamah — Botswana
56) Hamza Mohammed Salau — Iran (Tehran)
57) Ibrahim Danlami — Kenya
58) Ibrahim Adeola Mopelola — Benin (Cotonou)
59) Ayeni Adebayo Emmanuel — Belgium (Brussels)
60) Akande Wahab Adekola — Switzerland (Berne)
61) Arewa Esther — Namibia (Windhoek)
62) Gergadi Joseph John — Gabon (Libreville)
63) Luther Ogbomode Ayo-Kalata — Sierra Leone
64) Danladi Yakubu Nyaku — Sudan (Khartoum)
65) Bello Dogon-Daji Haliru — Thailand (Bangkok)
Onanuga ya kara da cewa tuni Birtaniya ta amince da nadin Aminu Dalhatu a matsayin Babban Kwamishina, sannan Faransa ta amince da nadin Ayodele Oke a matsayin jakada.
Karanta:Gwamnan Katsina ya yaba da karin girman mukamin Masari
Har yanzu kuma an aika sunayen sauran jakadu 62 zuwa kasashen da za su je domin jiran amincewa da nadinsu.
Recent:INEC ta karyata sanarwar dake cewa masu rike da mukmai su yi murabus don shiga zaɓen 2027
