Farashin ɗanyen mai ya tashi da kashi goma cikin ɗari yayin da kasuwannin makamashi a Asiya suka buɗe a ranar Litinin, ƙari mafi yawa da aka samu tsawon watanni.
Wannan yana nuna haɗarin da ke tattare da jigilar mai ta Mashigin Hormuz da Iran ta ba da sanarwar rufewa.
Tuni ƙasashen duniya suka fara shirin tunkarar sakamakon da ke tattare da hakan, la’kari da cewa ta nan ne ake wucewa da aƙalla kashi 20 cikin 100 na makamashin da ake amfani da shi a duniya ciki har da man fetur.
Rahotanni sun ce dakarun sojin ruwan Iran na kai hari kan dukkan jiragen ruwan da suka nemi kangarewa umarninsu na ja da baya, harma sun lalata wasu jiragen dakon mai uku.
Kasuwannin hannayen jari da suka buɗe da safiyar nan a Asiya sun fadi warwas. Akwai fargabar cewa rikicin da ke ci gaba da faruwa zai iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya.
Karanta:Iran ta naɗa Alireza Arafi jagoran addinin ƙasar na riƙo
