Ofishin hukumar kare hakkin bil’adama ta International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC–RFT) a Najeriya ya fitar da sanarwar gaggawa dangane da lamarin Walida Abdullahi, wadda aka rawaito cewa an ɗauke ta tana ƙarama, aka riƙe ta na wani tsawon lokaci, lamarin da ake zargin ya jefa lafiyarta da walwalarta cikin haɗari.
A cikin sanarwar da Daraktan ƙasa na ƙungiyar, Ambasada Abdullahi Bakoji Adamu, ya sanya wa hannu, IHRC–RFT ta bayyana cewa batun ya shafi haƙƙin ɗan Adam da kariyar yara, ba wai na addini, siyasa ko yanki ba.
Ƙungiyar ta jaddada muhimmancin bin doka da fifita muradin yaro a kowane mataki.
Ƙungiyar ta buƙaci da a maido da Walida ga iyayenta nan take, ko kuma a sanya ta a wuri mai tsaka-tsaki ƙarƙashin kulawar kotu har sai an kammala shari’a.
Haka kuma ta nemi a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa cikin gaskiya ba tare da son zuciya ba, tare da mutunta duk wani ingantaccen umarnin kotu ba tare da ɓata lokaci ba.
IHRC–RFT ta yi nuni da cewa dokokin da suka tanadi kariya ga ɗan Adam sun fito fili a cikin Universal Declaration of Human Rights da kuma kundin tsarin mulki na Najeriya waɗanda suka tabbatar da haƙƙin rayuwa, mutunci, ‘yanci da kariya daga tsarewa ba bisa ka’ida ba.
