Wasu ‘yan bindiga sun ƙone sansanin sojoji da motocinsu biyu a ƙauyen Bagega da ke Anka a jihar Zamfara a ranar Asabar.
Masu mazauna garin da sojoji biyu sun ji rauni a lokacin harin da ‘yan ta’addan suka kai waɗanda suka sace wa mutane kayayyaki a shagunansu.
Mazaunan sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa, ‘yan ta’addan sun so su tashi kasuwar Bagega da ake ci ne a ta mako-mako ne, amma sojojin da suke zaune a ƙauyen sun yi fito-na-fito da su inda aka kwashe awa biyu ana ba-ta-kashi kafin ‘yan ta’addan su gudu sakamakon ƙarin sojoji da suka zo daga cikin garin Anka.
“Sojoji sun yi nasarar murƙushe ‘yan bindiga a ƙoƙarin da suka fara yi. Ba su san akwai jami’an tsaron da suke sintiri a wajen ƙauyen ba. ‘Yan bindigar sun fito ne daga Sunke da sauran ‘yankuna.”
“Da misalin ƙarfe 1 na rana, sai muka fara jin harbe-harben bindiga daga wajen garin. Nan da nan sojoji suka ɗauki ababen hawansu suka nufi garin doomin su tunkari ‘ya bindigar,” a cewar wani basarake wanda ya nemi a sakaya sunansa a yayin zantawa da PREMIUM TIMES.
Mazauna garin sun ce harbe-harben bindigar ne ya tilasta wa mutane guduwa daga kasuwar.
“’Yan bindigar sun fito ne da yawansu. Za ka iya jin ƙarar harbe-harben bindiga daga kowanne ɓangare,” in ji wani ganau da ke zaune a garin.
“’Yan bindigar sun shiga kasuwa inda suka sace wayoyin mutane da lemukan. Ba shakka da suka ɗaga wa ƙafa. Duk sai da suka yi musu sata,” in ji Sadiq Sulaiman, wani mazaunin Bagega.
karanta:‘Yanbindiga sun kashe ɗan kasuwa sa’o’i kafin bikin sunan dansa a Edo
Mazauna garin da dama sun ji rauni a yayin harbe-harben bindigar. Izuwa yanzu, ba mu da adadin fararen hular da aka kashe.
Sarakunan sun ce sojoji biyu sun ji rauni a yayin da ake kyautata zaton kashe ‘yan bindiga da dama.
Mai magana da yawun rundunar Fansan Yamma (2 JTF) Olaniyi Osoba, bai amsa saƙon kar-ta-kwana da na WhatsApp da muka aika masa ba kan harin.
Bagega, garin ‘yan kasuwa ne da ke kusa da dajin Sunke da Bagega, dazukan da ake amfani da su wajen muzguna wa al’ummar Kebbi da Neja da kuma garuruwa kamar Maru da Bukkuyum.
Bagega da sauran garuruwan da ke kewaye suna da albarkatun gwal da sauran albarkatun ƙasa wanda ke jawo musu ‘yan ta’adda da ke da sansanoninsu a dazukan da ke garuruwan Bagega.
Garuruwan da ke yankin Arewacin Najeriya suna fama da samamen ‘yan ta’adda tun kusan shekarun 2011 wanda ya jawo mutuwar ɗaruruwan mutane da raba miliyoyin mutane da gidajensu.
Wannan tashe-tashen hankula sun shafi al’umma da kuma tattalin arziƙin na ƙasa
Recent:Ƴan Nijeriya 62 na tsare a Uganda kuma an hana su ganawa da lauyoyi
