Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana damuwa kan yadda ake samun karuwar hare-hare kan jiragen kasa a layin Abuja–Kaduna.samun karuwar hare-hare kan jiragen kasa a layin Abuja–Kaduna.
Hukumar ta bayyana damuwarta ne bayan wani sabon hari da aka kai wa jirgin kasan, inda aka jefi jirgin da duwatsu aka fasa gilashin gaban injinsa.
Ta kara da cewa, lamarin ya faru ne bayan wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka taru suna jifan jirgin a yayin da yake tafiya da fasinjoji a cikinsa.
Irin waɗannan hare-hare sun karu a makonnin baya-bayan nan, inda aka samu sama da sau shida a wurare daban-daban a wannan hanya, a cewar Hukumar ta NRC.
karanta:APC’s Strength Lies in Cohesion, Discipline — 2027 Presidential Aspirant Maidoya
Ta ce lamarin na da matukar hatsari, domin yana barazana ga lafiyar fasinjoji, ma’aikatan jirgin kasa da kuma muhimman kayayyakin gwamnati.
Duk da haka, ta ce ana ci gaba da kara tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da lafiyar matafiya a yayin da take ci gaba da jigilar fasinjoji a kan hanyar.
Ta kuma ce tana aiki tare da jami’an tsaro da shugabannin al’umma domin gano wadanda ke da hannu a wannan lamari da kuma daukar matakin doka a kansu.
Hukumar ta bukaci al’ummomin da ke zaune a kusa da layin jirgin kasa da su taimaka wajen kare kayayyakin gwamnati ta hanyar bayar da rahoton duk wani abu mai kama da barazana.
Ta yi gargadi cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba, hare-haren na iya kawo cikas ga ayyukan jirgin kasa a nan gaba.
Recent:2027 Elections: Shinkafi Declares Zamfara North Senatorial Bid
