Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
An kashe basaraken ne a ƙauyen Ochia, inda aka kuma ƙone gawarsa, lamarin da ya ƙara tayar da hankali a yankin.
Jami’an rundunar ’yan sandan Jihar Imo sun bazama wajen farautar waɗanda suka kashe wani basaraken gargajiya a Karamar Hukumar Ohaji/Egbema.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe basaraken ne a ƙauyen Ochia, inda aka kuma ƙone gawarsa, lamarin da ya ƙara tayar da hankali a yankin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Henry Okoye, ya ce sun samu kiran gaggawa a ofishinsu na Ohaji a ranar Juma’a, wanda ya kai ga tura jami’ai wurin da abin ya faru a yankin Assa.
karanta:Dalilan da su ka sanya ba mu cimma matsayar tsagaita wuta ba – Iran.
Ya ce da isar jami’an, sun tarar da cewa an riga an ƙone gawar basaraken, amma daga bisani aka tattaro ragowar tokar aka kai ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Owerri (FUTH) domin gudanar da bincike.
Okoye ya ƙara da cewa kwamishinan ’yan sanda Audu Garba Bosso ya ba da umarnin a gudanar da bincike mai zurfi ba dare ba rana domin gano masu hannu a wannan ɗanyen aiki, tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban kotu.
Ya jaddada cewa duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aika ba zai kuɓuta daga hukunci ba, yana mai cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’in ta’addanci ba.
Haka kuma, rundunar ta buƙaci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai, musamman wajen bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen cafke masu laifi.
Recent:Kwastam ta kama ƙwayar tramadol da sauran miyagun ƙwayoyi na kimanin N1.05bn a Edo.
