Daga Sani Adamu Hassan
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, sun bayyana goyon bayansu ga Rabiu Suleman Bichi domin ya zama mataimakin gwamnan jihar.
Jaridar Punch ta rawaito cewa hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Tsare-tsare na kungiyar APC Legacy Group, Indo Albarka, ya fitar a ranar Litinin a Abuja.
Albarka ya bayyana cewa zabin Bichi wata dabara ce ta ƙarfafa hadin kai a cikin jam’iyyar, musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Sanarwar ta ce Abdullahi Abbas ne ya gabatar da kudirin goyon bayan Bichi a wani taron masu ruwa da tsaki, yayin da Mataimakin Shugaban jam’iyyar a jihar, Salisu Gwangwazo, ya mara masa baya.
karanta:ADC Inaugurates New Bauchi Leadership, Dankama Pledges Unity, Electoral Repositioning
A cewar sanarwar, shugabannin jam’iyyar na ganin fitowar Bichi na da matukar muhimmanci wajen karfafa hadin kan APC a Kano, musamman kafin tunkarar zabukan gaba.
Game da kwarewarsa, kungiyar ta bayyana Bichi a matsayin gogaggen dan siyasa mai cikakken gogewa a matakan gwamnati daban-daban.
Ta ce ya taba rike mukaman Darakta Janar na Bankin Raya Birane na Najeriya, Darakta Janar na KNUPDA, Kwamishina, da kuma Sakataren Gwamnatin Jiha a gwamnatoci biyu.
