Daga Mustapha Abdullahi
Babbar alkaliyar kotun kare haƙƙin bil’adama ta Afirka (AfCHPR), Stella Isibhakhomen Anukam ta yi kira da a zage dantse wajen kare hakkin dan adam a Afrika, maimakon a rika fada da baki ba tare da wani aiki a fili ba.
Anukam ta fadi haka a maƙalar da ta gabatar a yayin bikin cikas AfCHPR shekaru 20 da kafuwa da Jami’ar Baze da ke Abuja ta karbi bikin na bana a ranar Alhamis.
A maƙalar, mai taken “ mu gani a ƙasa ba wai alkawura ba” – duba akan shekaru 20 na aikin kare hakkin dan adam, Anukam ta yi taza da tsifa akan nasarorin da kotun ta samu wajen kwato hakkunan al’umma a Afirka.
Ta kuma nuna muhimmancin aiki da jiki maimakon maganganu na farar baki da ba kasafai ake cika su ba, inda ta kuma bayyana irin nasarorin da kotun ta samu wajen kare hakkin dan adam da kuma tsare-tsare da ta kawo na Shari’ah akan kare hakkin bil’adama a kasashen da suke mambobi a kotun.
Taron, wanda aka gudanar a tsangayar ilimin Shari’a na jami’ar Baze, ya samu halartar malaman jami’o’i da lauyoyi da masu rabon kare hakkin bil’adama da dalibai da sauran su.
Haka su ma malaman jami’ar, a nasu jawaban, sun fito da amfanin karfafa alaƙa da ƙungiyoyin rajin kare haƙƙin bil’adama da nufin karfafa tanade-tanden shariah.
Recent:Allah-wadai da Kashe Shanu Takwas a Karamar Hukumar Bassa, Jihar Filato.
