Daga Mustapha Abdullahi
Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta yaba da ziyarar da Shugaban Jam’iyya ta ƙasa ya kai jihar, ta bayyana ziyarar a matsayin wani babban abin ƙarfafa haɗin kai da ƙara wa mambobi ƙwarin gwiwa.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jihar, Kwamared Auwalu Abdullahi Soja ya fitar, jam’iyyar ta ce ziyarar ta yi tasiri ga mambobinta a faɗin jihar, inda ta ƙarfafa haɗin kai tare da sabunta amincewa da shugabancin jam’iyyar.
Karanta:2026 World Health Day: Bauchi Reaffirms Commitment to Science-Driven Healthcare
Sanarwar ta kuma yaba da yadda Shugaban Jam’iyyar na ƙasa ya kai ziyara ga tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Sanata, Malam Ibrahim Shekarau, da kuma fitaccen ɗan siyasa, Sanata Bello Hayatu Gwarzo.
Sanarwar ta kara da cewa ga mambobin APC din, waɗannan mu’amaloli na nuna ƙuduri mai ƙarfi na gina kyakkyawar alaƙar siyasa da kuma ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar.
APC ta Kano ta sake jaddada buɗaɗɗiyar ƙofarta ga duk masu sha’awar shiga jam’iyyar, tare da tabbatar da cewa tana shirye ta yi aiki da duk masu ruwa da tsaki domin cigaba da bunƙasar jam’iyyar a fadin jihar.
Recent:World Health Day: Bauchi Health Officials Promote Awareness, Digital Healthcare Among Student Nurses
