Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Amurka da Iran sun bayar da dalilai masu cin karo da juna, a matsayin abin da ya sa aka gaza cimma matsaya a zaman tataunawar zaman lafiya da ƙasashen biyu su ka yi a Pakistan.
Karanta:Allah-wadai da Kashe Shanu Takwas a Karamar Hukumar Bassa, Jihar Filato.
Shafin BBC Hausa na X ya rawaito cewa kafar yaɗa labaran gwamnatin Iran, IRIB ta ruwaito cewa an gaza cimma yarjejeniyar zaman lafiya a taron na birnin Islamabad ne saboda wasu “buƙatu marasa amfani” da Amurka ta gabatar.
“Duk da ƙoƙarin da wakilan Iran suka yi domin ganin komai ya tafi yadda ya dace, wasu ”buƙatu marasa amfani” daga ɓangaren Amurka sun sa an gaza ƙulla yarjejeniya. Da haka zaman tattaunawar ya tashi,” in ji kafar yaɗa labarai ta IRIB a wani saƙo da ta wallafa a Telegram.
Amma Amurka ta ce buƙatun nata “masu sauƙi” ne kuma “waɗanda su ka dace”.
Recent:Ya kamata a zage dantse wajen kare haƙƙin ɗan adam a Afirka – Anukam
