Reshen Jihar Filato na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya yi watsi da ikirarin da Mataimakiyar Shugabar Mata ta Yankin Zonal ta Ƙasa, Hannatu Gagara, ke yi na neman kujerar Shugabar Jam’iyyar a jihar, yana mai bayyana hakan a matsayin yaudara da rashin girmamawa ga shugabancin jam’iyyar da aka kafa bisa ƙa’ida.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na jiha, Silas Audu Wettok, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce ikirarin Gagara ba ya nuna hakikanin abin da ke faruwa a cikin jam’iyyar, kuma yana tauye tsarin mulkinta.
Jam’iyyar ta kuma yi Allah-wadai da kalaman da ake zargin Gagara ta yi kan tsohon Minista kuma jigo a jam’iyyar, Solomon Dalung, wanda ta bayyana a matsayin “mai kawo cikas.” ADC ta bayyana kalaman a matsayin marasa dacewa, tare da zarginta da neman daukar hankali ba tare da wani dalili ba.
Karanta:Sai da aka yi min tiyata a makogwaro bayan hira da Al Jazeera – Bwala.
Da take sake jaddada kudirinta na tabbatar da dimokuraɗiyyar cikin gida, jam’iyyar ta bai wa mambobinta da al’umma tabbacin shirinta na gudanar da sahihai kuma ingantattun tarukan jam’iyya a faɗin Jihar Filato. Ta kara da cewa Kwamitin Babban Taron Jam’iyyar na Ƙasa na sa ido kan tsarin domin tabbatar da bin ƙa’idojin da aka gindaya.
Sanarwar ta kuma zargi wasu ‘yan siyasa da katsalandan, tana mai cewa “masu neman mulki cikin matsananciyar sha’awa” na kokarin kafa wata shugabanci ta daban bayan sun rasa goyon bayan jama’a. Ta gargadi cewa za a fallasa duk masu hannu a kokarin tayar da zaune tsaye a cikin jam’iyyar.
Domin kare sahihancin tarukan jam’iyyar, ADC ta bayyana cewa Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa ya nada jami’an tuntuba a faɗin ƙasar. A Jihar Filato, an naɗa Rhoda Sanda Daniels a matsayin kadai mai ikon rabawa da karɓar fom ɗin tsayawa takara. Jam’iyyar ta gargadi cewa duk wani fom da aka samu daga wata majiya dabam za a ɗauke shi a matsayin mara inganci.
Jam’iyyar ADC ta yi kira ga mambobinta da sauran jama’a da su kasance masu lura tare da kauce wa ruɗewa, tana mai jaddada kudirinta na samar da ingantaccen shugabanci da tsare-tsaren siyasa masu gaskiya da riƙon amana.
Recent:Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon taya murna ga Alhaji Aliko Dangote,
