Daga Sani Adamu Hassan
Wasu manyan jagororin jam’iyyar ADC na shirin ficewa zuwa jam’iyyar NDC , yayin da tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, ke cikin masu nazarin wannan mataki kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito.
Rahotanni sun nuna cewa rashin gamsuwa da tsarin cikin gida na ADC da kuma rikicin shugabanci da ke gaban kotu sun sa wasu jiga-jigan jam’iyyar sake duba matsayinsu. Duk da hukuncin Kotun Koli ya dawo da shugabannin jam’iyyar na wucin gadi, har yanzu ana ci gaba da shari’ar a babbar kotu, lamarin da ke haifar da fargaba.
Majiyoyi sun ce Obi na tattaunawa da masu ruwa da tsaki, inda ake zargin cewa NDC ta yi masa alkawarin tikitin takarar shugaban kasa ba tare da kalubale ba idan ya koma cikinta.
karanta:Kasar Iran zata buga wasannin FIFA a Amurka duk da yakin da ake yi
Sai dai jami’in kungiyar magoya bayan Obi, Yunusa Tanko, ya ce ba zai tabbatar ko musanta shirin ba, amma ya jaddada cewa Obi zai tsaya takara a 2027.
A bangaren NDC, an bayyana cewa ana tattaunawa da Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, tare da yiwuwar ba su damar samun tikitin takara, yayin da jam’iyyar ke maraba da su.
Haka kuma, wasu shugabannin ADC na ci gaba da nazarin komawa NDC, suna mai cewa rikicin cikin gida da shari’o’i na iya raunana jam’iyyar kafin zabe.
A wani bangare, tsohuwar ‘yar takarar gwamnan Adamawa, Sanata Aishatu Binani, ta fice daga ADC tare da komawa NDC, inda ta ce ta yanke shawarar ne bisa ra’ayin magoya bayanta da kuma tsarin jam’iyyar.
Sai dai kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya musanta rahoton cewa shugabannin jam’iyyar na shirin ficewa, yana mai cewa ba shi da masaniya kan hakan.
Recent:2027: PDP a Kogi ta amince da tikitin takara kai tsaye ga Natasha
