Daga Mustapha Abdullahi
Shugabancin na jam’iyyar PDP a Jihar Kogi ya amince da bai wa Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, tikitin takara kai tsaye domin sake tsayawa takara a zaben 2027.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa an yanke wannan hukunci ne a wani taro da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Lokoja, inda aka tabbatar da shawarar da shugaban jam’iyyar na jihar, Muhammed Gambo, ya gabatar tun da farko.
Jam’iyyar ta kuma tabbatar da Natasha a matsayin jagorar PDP a jihar, tana mai yabawa gudunmawar da take bayarwa ga jam’iyyar da kuma ayyukan ci gaba da ta aiwatar a mazabarta.
Gambo ya jinjinawa yadda take wakilci a Majalisar Dattawa, yana mai cewa ta kawo cigaba ta hanyar shirye-shiryen tallafa wa al’umma, gine-ginen makarantu da kasuwanni, samar da gidaje da kuma horas da jama’a sana’o’i.
Jam’iyyar ta bayyana cewa ita ce zabin kowa don takarar sanatan Kogi ta Tsakiya a 2027, tare da tabbatar mata da cikakken goyon baya.
Rahotanni sun nuna cewa Natasha ta sanar da aniyarta ta sake tsayawa takara ne bayan tuntuba da matsin lamba daga al’ummar mazabu biyar da take wakilta.
Recent:Kasar Iran zata buga wasannin FIFA a Amurka duk da yakin da ake yi
