Kungiyar Malaman Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero, a Jihar Kebbi za ta tsun duma fage yajin aikin gama-gari na dindindin idan har gwamnatin jihar Kebbi ta kasa biyan hakkokin mambobinta.
An bayyana matsayin kungiyar ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar 22 ga Afrilu, 2026, a sakatariyar ASUU-AFUSTA da ke Aliero.
Sanarwar da aka fitar a wajen taron na dauke da sa hannun shugaban reshen Kungiyar na Jami’ar Dakta Musa Isah Fakai da sakataren Kungiyar Dakta Gado Abubakar A. A jawabin da ta yi wa manema labarai a wajen taron, ASUU-AFUSTA ta ce ya zama wajibi a sanar da jama’a da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi kan matsalolin da suka dabai baye Jami’ar suka kuma kawo cikas ga harkokin ilimi a Jami’ar sama da shekaru goma.
Karanta:Manoman shinkafa sun koka kan karuwar shigo da ita daga waje
“Haka kuma, ya zama jawabi ga jama’a da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi a Jihar Kebbi domin yin kira ga hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakan da suka dace don magance matsalar ’yan kwadago da ta addabi Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio, da ke a karamar hukumar Aliero,” in ji kungiyar.
Kungiyar ASUU-AFUSTA ta ruwaito Gwamna Nasir Idris, wanda ta kira shi da “Comrade Dakta Nasir Idris (Kauran Gwandu),” inda ta ambato shi yana cewa, “mafi yawan nasarorin da ake samu ana samun su ne ta hanyar gudanar da aikin kwazo da kuma jajirce wa.
Recent:Bauchi Sabuwa Project Organises Preliminary Debate For Governorship Aspirants
