Wasu ‘yanbindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani ɗan kasuwa mai suna Justice Abu Oshioke, wanda shi ne Babban Daraktan kamfanin abinci na Principle Take Out Eatery and Restaurant, a garin Ekpoma da ke ƙaramar hukumar Esan West a Jihar Edo.
Rahotanni sun ce an harbe Oshioke mai shekaru 30 ne sa’o’i kaɗan kafin bikin suna na ɗansa. An ce ya fita ne domin karɓar wani oda na kayan bikin lokacin da maharan suka yi ƙoƙarin sace shi.
Karanta:2027 Elections: Shinkafi Declares Zamfara North Senatorial Bid
Majiyoyin ‘yansanda sun bayyana cewa mamacin ya koma gida ne domin ɗaukar wasu kayayyakin kasuwancinsa kafin a kai masa hari. Daga bisani an garzaya da shi wani asibiti da ke kusa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Edo, DSP Eno Ikoedem, ta ce binciken farko ya nuna cewa lamarin ya samo asali ne daga yunƙurin sace shi da bai yi nasara ba.
Ta ƙara da cewa kwamishinan ‘yansanda na jihar, Monday Agbonika, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike tare da ƙaddamar da farautar waɗanda suka aikata laifin.
Recent:ANA YAWAN SAMUN KARUWAR HARE-HARE KAN JIRAGEN KASA A LAYIN ABUJA–KADUNA. NRC
