Daga Mustapha Abdullahi
TsohonTsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ADC, yana mai danganta hakan da rikice-rikicen cikin gida da ke ƙara tsananta a jam’iyyar da kuma kalubalen da ƙasar ke fuskanta gaba ɗaya.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa ranar Lahadi a shafinsa na X, Obi ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan nazari mai zurfi da kuma raɗaɗin zuciya na shirun da ya dade yana ɗauke da shi yayin tafiyar da harkokin siyasa a Nijeriya.
Ya bayyana tsarin ƙasar a matsayin wanda ya ƙara zama mai guba, yana mai cewa ya cika da tsoratarwa, rashin tsaro, zargi da kuma sanyaya gwiwa, abubuwan da ya ce su kan zama tarnaki ga hidima mai inganci ga bunkasar jama’a.
Obi ya kuma ce ya fuskanci suka mara adalci da matsin lamba daga cikin muhallan siyasa da ya shiga domin neman haɗin kai da neman shugabanci mai cike da kishi na niyyar gyara.
karanta:Kwankwaso Na Duba Yiwuwar Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar NDC
Ya bayyana cewa ficewarsa daga ADC ba ta da alaƙa da wata matsala ta kai tsaye da shugabannin jam’iyyar, ciki har da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark ko tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, waɗanda ya ce har yanzu yana girmamawa.
A cewarsa, abin da ya sa ya ɗauki wannan mataki shi ne yadda rikice-rikicen siyasa da ba a warware ba, da kuma yawan shari’o’i da sabanin cikin gida suka mamaye jam’iyyar, har suna hana ta mayar da hankali kan muhimman batutuwan ƙasa.
Recent:Kwankwaso Ya Musanta Zargin Sauya Jam’iyya, Ya Ce Ba a Yanke Shawara Ba Tukunna
