Daga Sani Adamu Hassan
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bukaci magoya bayansa da su fice daga jam’iyyar ADC, yayin da yake shirin sauya sheka zuwa wata sabuwar jam’iyya mai suna NDC a mako mai zuwa.
Rahotanni sun ce wannan mataki na zuwa ne bayan Kwankwaso ya bar jam’iyyar NNPP zuwa ADC kwanaki kadan da suka gabata, lamarin da ke nuna saurin sauyin siyasa a bangarensa.
Karanta:Jagororin ADC da Peter Obi na duba yiwuwar komawa jam’iyyar NDC
Ana kuma sa ran cewa Kwankwaso zai koma NDC tare da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, wanda ake rade-radin shi ma zai sauya jam’iyya nan ba da jimawa ba.
Majiyoyi sun bayyana cewa akwai yiwuwar Kwankwaso da Obi su hada kai wajen tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027, karkashin wata hadakar tikitin siyasa.
Jaridar Manuniya ta rawaito cewa, ana sa ran ‘yan majalisar da suka bar NNPP zuwa ADC za su sanar da ficewarsu domin komawa NDC tare da Kwankwaso. Ana kuma tattaunawa da wasu daga cikin ‘yan majalisar da suka bi sahun Obi zuwa ADC kan yiwuwar sauya sheka zuwa sabuwar jam’iyyar.
Recent:Ina nan a kan matsayina na takarar Sanata babu gudu babu ja da baya-Yusuf Zailani
