Daga Sani Adamu Hassan
Dan takarar kujerar Majalisar Dattawa daga Kaduna ta Tsakiya Honorabul Yusuf Zailani, ya tabbatar da cewa yana nan daram a cikin fafatawar siyasa, yana mai cewa kudurinsa na tsayawa takara bai sauya ba.
karanta:2027: PDP a Kogi ta amince da tikitin takara kai tsaye ga Natasha
A cikin wata sanarwa, dan takarar ya bayyana cewa jajircewarsa wajen yi wa al’ummar yankin hidima na kara karfi a kowane lokaci, tare da jaddada aniyarsa ta wakiltar muradunsu a matakin kasa.
Ya kuma gode wa al’ummar yankin bisa irin gagarumin goyon baya, addu’o’i da amincewar da suke ci gaba da nuna masa, yana mai cewa wannan ne yake kara masa kwarin gwiwa, ba wai wasu goyon baya na musamman ko ra’ayoyi na wucin gadi ba.
Dan takarar ya kara da cewa yana da yakinin cewa, da yardar Allah, muradin jama’a ne zai yi rinjaye a zaben da ke tafe.
Ya ce yana nan a shirye domin samar da ingantattun dokoki da za su amfani al’ummar Kaduna ta Tsakiya, yana mai bayyana kansa a matsayin gogaggen dan majalisa da ya shafe sau biyar yana wakiltar jama’a.
A karshe, ya jaddada shirinsa na tsayawa takarar Majalisar Dattawa tare da alkawarin kawo dokoki masu inganci idan aka zabe shi.
Recent:Jagororin ADC da Peter Obi na duba yiwuwar komawa jam’iyyar NDC
