Wata kafar yaɗa labarai ta rawaito cewa jirgin na ɗauke da fasinjoji daga Azuzuama a ƙaramar hukumar Southern Ijaw, kuma ya kife ne a yankin Ikebiri-1 da misalin ƙarfe 1 na dare ranar Laraba, yayin da yake kan hanyarsa zuwa Yenagoa, babban birnin jihar.
Rahotanni sun nuna cewa an gano gawarwakin yaran — maza biyu da mace ɗaya, masu shekaru tsakanin shida zuwa 15 a cikin ruwa ta hannun wasu kwarawa na yankin, sannan aka mayar da su Azuzuama, inda suka fito.
Tsohon shugaban ƙungiyar ma’aikatan jiragen ruwa a Bayelsa, Ipigansi Ogoniba, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun aika da masu nutsewa daga Yenagoa domin taimakawa, kuma suna jiran cikakken rahoto.
Karanta:Bauchi Sabuwa Project Organises Preliminary Debate For Governorship Aspirants
Har yanzu ba a san adadin fasinjojin da ke cikin jirgin ba, domin jirgin bai tashi daga Yenagoa ba. Ana zargin cewa hatsarin ya faru ne saboda lodin da ya yi yawa da kuma lalacewar na’urar fitar da ruwa daga cikin jirgin.
Daily Trust ta ce.da ta tuntubi kakakin ‘yan sanda na jihar, DSP Musa Muhammad, ya ce bai samu labarin faruwar lamarin ba, amma ya yi alkawarin bincike — sai dai bai sake bada wani bayani ba bayan haka.
Recent:Kungiyar Malaman Jami’ar AFUSTA Za Ta Tsunduma Yajin Aiki.
