Akalla ‘yan Najeriya 62 ne ke tsare a ƙasar Uganda, inda ake zargin hukumomin ƙasar sun hana su damar ganawa da lauyoyinsu.
Rahotanni sun nuna cewa an kama mutanen ne a yankunan Adjumani da Kampala bisa zargin gudanar da ayyukan coci ba tare da izini ba.
Sai dai shugabansu, Michael ChristisKing, ya musanta zargin, yana mai cewa su ‘yan mishan ne da ke gudanar da ayyukan jin kai, kuma sun bi dukkan ƙa’idoji kafin shiga ƙasar.
Karanta:ANA YAWAN SAMUN KARUWAR HARE-HARE KAN JIRAGEN KASA A LAYIN ABUJA–KADUNA. NRC
Wani lauya mai suna Israel Mivule, wanda ke wakiltarsu, ya bayyana cewa an hana shi damar ganawa da waɗanda ake tsare da su, duk da kasancewarsa lauyansu. Ya ce hakan ya saba wa dokokin Uganda da ke tabbatar da ‘yancin samun lauya da kuma shari’a mai adalci.
Haka kuma, an ce an hana waɗanda ake tsare da su damar sadarwa da iyalansu da kuma lauyoyinsu.
A halin yanzu, ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an sako mutanen ta hanyar diflomasiyya, yayin da ake hasashen cewa za a iya kai ƙarar lamarin zuwa kotu idan ba a samu mafita cikin gaggawa ba.
Recent:‘Yanbindiga sun kashe ɗan kasuwa sa’o’i kafin bikin sunan dansa a Edo
