Daga Mustapha Abdullahi
Ya ba sojoji tabbacin cigaba da tallafawa ayyukansu da ƙarfafa musu gwiwa don Samar da Tsaro.

A wata ziyara ta ba-zata zuwa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a madadin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa ta’aziyya ga Rundunar Sojin Nijeriya da gwamnatin Jihar Borno kan hare-haren baya-bayan nan da suka yi sanadiyyar mutuwar Birgediya Janar Oseni Braimah da wasu jami’ai na rundunar.
Karanta:Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon taya murna ga Alhaji Aliko Dangote,
Yayin da yake nuna girmamawa ga sadaukarwar Rundunar Sojin Nijeriya, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce:
“Waɗannan mutane sun sanya kayan soja ne domin kare mu duka. Sun tsaya wajen kare al’ummominmu, iyalanmu, da makomar ‘ya’yanmu. Jarumtarsu na tuna mana cewa zaman lafiya da tsaro sau da yawa na zuwa da tsada mai girma ƙwarai.”
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma ba da tabbacin cigaba da tallafin Gwamnatin Tarayya, yana mai cewa masu aikata laifuka ba za su samu mafaka ba a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
