Wanda ya kafa jam’iyyar NNPP, Dr Boniface Aniebonam, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta yi amfani da tsarin sasanci (consensus) wajen zaɓen ‘yan takararta a zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a Lagos, Aniebonam ya ce jam’iyyar ta yi afuwa ga dukkan mambobin da aka kora a baya, tare da ba su damar komawa cikin jam’iyyar.
Ya kuma tabbatar da cewa za a bai wa dukkan mambobin NNPP da ke riƙe da mukaman gwamnati tikitin takara kai tsaye a zaɓen 2027, kamar yadda aka yanke a taron ƙoli na jam’iyyar.
Karanta:Ƴan Nijeriya 62 na tsare a Uganda kuma an hana su ganawa da lauyoyi
Shugaban ya ce tsarin sasanci zai taimaka wajen fitar da ƙwararrun ‘yan takara maimakon siyasar kuɗi, inda ya buƙaci masu sha’awar shiga takara, musamman mata, da su fito, yana mai cewa za a rage musu kuɗin fom.
Haka kuma, ya umarci tsoffin mambobin da ke son dawowa su gabatar da kansu ga shugabancin jam’iyya ƙarƙashin Dr Agbo Major domin yin alkawari da biyayya.
Aniebonam ya ƙara da cewa waɗanda suka koma wasu jam’iyyu sakamakon rikice-rikicen cikin gida za su iya dawowa, amma dole su bi ƙa’idojin dokar zaɓe ta INEC, wadda ba ta amince da zama mamba a jam’iyyu biyu a lokaci guda ba.
Ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da sa ido kan harkokin jam’iyyar bisa hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ke Owerri, tare da kira ga sabbin mambobi da su shiga jam’iyyar domin cimma burin sabuwar Najeriya.
Recent;Yan ta’adda sun ƙone sansanin sojoji da motocin yaki a Zamfara.
