Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane hudu ‘yan gida daya a kauyen Geko dake karamar hukumar Riyom a jihar Filato.
Maharan sun kashe wani fasto Ayuba Choji, matarsa Chundung da ‘ya’yan su biyu Cyril da Endurance.
Mazauna kauyen sun ce maharan sun afka kauyen da misalin karfe 12 na daren Lahadin da ya gabata inda suka shigo suna ta harbi ta ko ina.
Wani mazaunin kauyen Martha Dalyop ya bayyana wa jaridar ‘Channels’ cewa harbe-harben bindigan da maharan suka rika yi bayan sun shigo kauyen ya firgida mutane inda hakan ya sa mutane neman mafaka cikin dazuka.
“Sun shigo kauyen cikin dare yayin da suke harbi ta ko ina inda dole mutane sun fito domin guje wa harin.
Wasu dattawa a kauyen sun ce akwai alamun yin shiri na musamman kafin maharan suke kai wa mutane hari a kauyen.
Kakakin kungiyar matasan Berom Rwang Tengwong ya ce mafi yawan lokuta maharan na taruwa da yawan kafin suke kai wa mutane hari a kauyuka inda da zaran sun shiga kauyen suke raba kansu biyu inda rabi ke kai wa mutane hari sannan sauran na lalata gonakin mutane.
“Ga dukan alamu maharan na yin shiri na musamman kafin suke kawo wa mutane hari domin da zaran sun shigo kauyen suke raba kan su gida uku inda rabi na kai wa mutane hari wasu na lalata gonakin mutane sannan sauran na yin gadi hanyoyi domin hana hana mutane samun dauki.
karanta:Gwamna Abba ya magantu kan zargin rabon tallafin “dan kamfai” ga mata a lokacin ziyarar Remi Tinubu
Tengwong ya ce a tsakanin sa’o’i 48 mahara sun lalata gonaki da dama dake Barkin Ladi da wadanda ke Kassa sannan amfani gona da suka hada kabeji, barkono, masara na daga cikin abincin da aka lalata.
Wannan harin ya faru bayan harin da mahara suka yi a kananan hukumomin Bokoos, Barkin Ladi da Jos ta Arewa inda mutane da dama suka rasa rayukan su.
A Riyom da kewaye mutane da dama sun rika kokawa da yawan kawo musu hari da mahara ke yawan yi inda a dalilin haka mutane da dama suka talauce.
Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnati da ta mike tsaye wajen inganta tsaro tare da daukan matan da za su tabbatar da tsaro.
