Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Akalla mutane takwas ne aka tabbatar sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da aka kai cikin dare a ƙauyen Mbwele da ke gundumar Kwatas, a ƙaramar hukumar Bokkos.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:45 na dare ranar 9 ga Afrilu, 2026, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kutsa cikin al’ummar, suka buɗe wuta tare da ƙona gidaje, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici.
An bayyana sunayen waɗanda suka rasu kamar haka: Habila Istifanus (38), Hassan Istifanus (31), Iliya Mangut (70), Sunday Gideon (31), Innocent Banabas (20), Lucky Titus (38), Wisdom Lucky (15), da Bwehsun Hassan (25).
Dukkan waɗanda abin ya shafa, ciki har da waɗanda suka jikkata, an kai su Asibitin Cottage na Bokkos domin samun kulawar lafiya bayan harin.
Ƙauyen Mbwele, wanda ke cikin unguwar Kwatas, bai wuce tafiyar mintuna 30 daga garin Bokkos ba, lamarin da ya haifar da damuwa a tsakanin mazauna yankin kan jinkirin kai ɗauki daga jami’an tsaro.
Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakin da ya dace, yayin da fargaba ke ci gaba da addabar al’umma sakamakon wannan hari.
Wannan lamari ya sake ƙara tayar da hankula kan matsalar tsaro da ke ci gaba da addabar wasu sassan jihar Filato, musamman a yankunan karkara.
Recent:A Tattauna Da Boko Haram Don Sako Mana Mutane 416 Da Aka Kama – Ƙungiya A Borno.
