Daga Mustapha Abdullahi Abubakar
Yan sanda a ƙasar Indonesia sun kama wasu mata biyu bisa zargin ɓatanci ga addini bayan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna ɗaya daga cikinsu tana taka Alƙur’ani.
Rahotanni sun ce matan, waɗanda ba a bayyana sunayensu ba, an kama su ne a Jihar Banten, kuma za su iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru har biyar a gidan yari idan aka same su da laifi ƙarƙashin dokar ɓatanci ga addini ta ƙasar.
Lamarin ya faru ne a wani shagon gyaran gashi a yankin Lebak, inda mai shagon ta zargi wata baƙuwa da satar kayanta.
Sai dai bayan matar ta musanta zargin, sai mai shagon ta tilasta mata yin rantsuwa tana taka Alƙur’ani, tare da ɗaukar bidiyon abin da ya faru.
Kakakin ‘yan sandan jihar, Maruli Ahiles Hutapea, ya ce matar da ta taka Alƙur’ani da kuma wadda ta tilasta mata sun amsa laifin da ake zarginsu da shi, kuma tuni aka sanya su cikin jerin waɗanda ake tuhuma.
Bidiyon wanda ya bazu a yanar gizo ya janyo fushin jama’a sosai, lamarin da ya ƙara tayar da ƙurar muhawara kan dokar ɓatanci ga addini a ƙasar.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun daɗe suna sukar irin waɗannan dokoki da suke ganin cewa ana amfani da su wajen tauye haƙƙin wasu ƙananan ƙungiyoyin addini.
Ana iya tuna cewa an taɓa ɗaure tsohon gwamnan birnin Jakarta, Basuki Tjahaja Purnama, kusan shekaru biyu a gidan yari a shekarar 2017 bisa irin wannan tuhuma.
Recent:Rikicin cikin gida na barazana ga APC a jihar Kano gabanin 2027
