Daga Mustapha Abdullahi
Kungiyar Makiyaya ta Ƙasa ta Nijeriya (MACBAN), reshen Jihar Filato, na yin Allah-wadai da kakkausar murya kan mummunan lamari mai tayar da hankali na kashe shanu takwas da ake zargin wasu matasan Irigwe ne suka aikata a Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
Wannan lamari ba wai kawai hari ne kai tsaye ga hanyoyin rayuwar makiyaya marasa laifi ba, har ma wani abu ne mai haɗari da zai iya ƙara rura wutar rikici da kuma rushe ƙoƙarin samar da zaman lafiya da ake yi a jihar.
Kiwo na daga cikin halattattun hanyoyin samun abin rayuwa ga dubban iyalai, don haka duk wani nau’in tashin hankali a kansa dole ne a ɗauke shi a matsayin babban laifi.
Muna kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta bincike kan wannan lamari tare da tabbatar da gano duk waɗanda ke da hannu a ciki da kuma gurfanar da su gaban kuliya. Dole ne a yi adalci cikin gaggawa domin kauce wa tangarɗar doka da oda, tare da kwantar da hankalin al’ummomin da abin ya shafa cewa ana kare musu haƙƙoƙi da dukiyoyinsu.
Kungiyar MACBAN ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin dukkan kabilu da rukunin sana’o’i a Jihar Filato. Muna kira ga mambobinmu da su kasance masu natsuwa da bin doka, yayin da muke ci gaba da tattaunawa da hukumomin da suka dace domin warware wannan matsala ta hanyoyin da suka dace.
Haka kuma muna kira ga shugabannin al’umma, ƙungiyoyin matasa da sauran masu ruwa da tsaki a Karamar Hukumar Bassa da su guji duk wani nau’in tashin hankali, su kuma rungumi hanyoyin warware rikice-rikice cikin lumana.
Gwamnatin Jihar Filato da duk masu ruwa da tsaki na tsaro su ɗauki matakai na gaggawa domin hana aukuwar irin wannan a gaba, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba tare da la’akari da asalinsu ba.
Zaman lafiya shi ne kawai hanyar da za ta kai ga ci gaba mai ɗorewa da haɗin kai a jiharmu mai daraja.
