Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon taya murna ga Alhaji Aliko Dangote, fitaccen ɗan kasuwa kuma shugaban Kamfanin Dangote bisa zagayowan ranar haihuwarsa.
A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai ya fitar, Shugaba Tinubu ya yaba da irin gudummawar da Dangote ya bayar wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da na Afirka baki ɗaya.
Karanta:2027: NBA ta gargadi lauyoyi da alƙalai kan tsoma baki a harkokin jam’iyyu
Shugaban Ƙasa ya jinjinawa hangen nesan kasuwanci na Dangote, jajircewarsa, kirkire-kirkirensa, da kuma jajircewarsa wajen samun nasara, waɗanda suka sauya fannoni daban-daban tare da ɗaga darajar Najeriya a matsayin cibiyar manyan masana’antu na Afirka.
Shugaban Ƙasa ya kuma yaba da ayyukan jin ƙai na Dangote, musamman ta hannun gidauniyar Dangote, waɗanda suka taimaka sosai a fannoni kamar lafiya, ilimi, da rage talauci.
A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya ba shi ƙarin lafiya, hikima, da kuma manyan nasarori a hidimar Najeriya, Afirka, da Kuma taimakawa wajen ayyukan jinkai
Recent:Sai da aka yi min tiyata a makogwaro bayan hira da Al Jazeera – Bwala.
