Daga Mustapha Abdullahi
Rahotanni sun bayyana cewa mazauna aƙalla kauyuka 21 a Jihar Sakkwato sun yi ƙaura daga gidajensu sakamakon hare-hare da barazanar ’yan bindiga da ke ci gaba da ƙaruwa.
Kauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Gidan Kare, Kaware, Chabi, Dattabi, Janwake, Sha Rana, Darbekami, Gidan Sule, Kuruwa, Mahuta, Dantayawa, Kawala, Bagirbe, Tsattsagi, Katsira, Imasa, Bela, Hura Girke, Galadimmai da Asha Ruwa.
Yawancin waɗanda suka tsere yanzu suna neman mafaka a garin Tureta da kewaye, inda suke fuskantar matsaloli na cunkoso, yunwa da rashin tallafi.
Wasu daga cikinsu suna zaune a gidajen ’yan uwa maimakon sansanonin gwamnati.
Karanta:Filato: Mutane 8 Sun Mutu, Wasu Sun Jikkata a Harin Bokkos.
Wani mazaunin yankin ya ce kwararar waɗanda suka tsere zuwa Tureta ta fara ne kusan kwanaki uku da suka gabata.
A halin yanzu, sama da mutum 1,000 suna kwana a makarantar firamare ta Abdulbaki Model a Tureta, inda ake cike a ɗakunan karatu ba tare da samun taimakon agaji ba.
Wani daga ƙauyen Kuruwa ya ce hare-haren da suka ci gaba da faruwa tun kafin watan azumin Ramadan ne suka tilasta musu barin gidajensu.
A Gidan Kare kuma, wani mazaunin ya bayyana cewa ana jin harbe-harbe kusan kowane dare, lamarin da ya jefa jama’a cikin tsananin tsoro.
Wani dattijo daga Bagirbe ya ce yawancinsu yanzu suna kwana a Tureta saboda tsoron hare-haren.
A Sha Rana, mazauna sun tsere a daren Alhamis bayan samun labarin cewa za a kai musu hari.
Wata uwa mai ’ya’ya huɗu daga Gidan Kare ta ce ’yan bindiga sun kashe mutane da dama kafin su tsere.
Wata mai juna biyu daga Hura Girke da ke zaune a makarantar firamaren, ta ce tana cikin mawuyacin hali saboda rashin abinci da tallafi, duk da cewa tana gab da haihuwa.
Dukkanin mazauna sun yi kira ga hukumomi da su kawo matakan tsaro cikin gaggawa domin su koma gidajensu da gonakinsu cikin zaman lafiya.
Sai dai ƙoƙarin jin ta bakin mai ba wa gwamnan Sokoto shawara kan harkokin tsaro, Kanar Usman Ahmad (ritaya), da kuma mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufai, bai yi nasara ba, domin ba su amsa kira da saƙonnin da aka tura musu ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.
