By mustapha Abdullahi Abubakar
Rahotanni sun ce wasu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun kai hare-hare biyu a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji 14, sannan wasu da dama suka jikkata.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa harin farko ya faru ne a daren ranar Talata a sansanin sojoji da ke garin Ngoshe a ƙaramar hukumar Gwoza.
A yayin harin, an kashe sojoji tare tare da wani limami da ke garin.
Wata majiyar soja da ta nemi a sakaya sunanta ta ce maharan sun tilasta wa sojojin janyewa daga sansanin, sannan suka kwashe wasu makamai da alburusai.
Har ila yau, sun yi garkuwa da wasu mata.
Bayan wannan harin, maharan sun sake kai wani hari a sansanin sojoji da ke Pulka, a Arewacin Gwoza.
A yayin wannan harin kuma sun kashe sojoji biyar ciki har da kwamandansu.
An kai sojojin da suka jikkata zuwa birnin Maiduguri domin samun kulawar likitoci.
Har zuwa yanzu rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
