Daga mustapha Abdullahi Abubakar
Dakarun rundunar 82 Division Garrison karkashin Operation Eastern Sanity sun kubutar da mutane 12 da aka sace a kauyen Ette da ke karamar hukumar Igbo-Eze North.

Al amarin ya faru ne ranar Juma’a 6 ga Maris 2026, bayan samun rahoton gaggawa cewa wasu ‘yan bindiga sun sace mazauna yankin.
Dakarun sojin tare da jami’an ‘yan sanda, masu gadin daji da kuma ‘yan Neighbourhood Watch sun kai farmaki wurin, lamarin da ya sa masu garkuwa da mutane suka tsere suka bar wadanda suka sace.

An kubutar da dukkan mutane 12 ba tare da sun ji rauni ba, sannan an kama mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin, kuma ana ci gaba da bincike.
Recent:An fara Rigakafin Cutar Zazzaɓin Cizon Sauro a Jihar Bauchi
