Daga Mustapha Abdullahi
ƘungiyarƘungiyar Borno South Youth Alliance (BOSYA) ta buƙaci gwamnatin tarayya da manyan jami’an gwamnati su shiga tattaunawa domin ceto mutane 416 da aka sace a Ngoshe, Jihar Borno, bayan da aka fitar da bidiyon da ke nuna cewa har yanzu suna raye.
A cikin wata sanarwa da shugabanta, Samaila Ibrahim Kaigama, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce ta shiga tattaunawa cikin sirri da masu garkuwa da mutanen bayan farmakin da suka kai wa yankin. Ta ƙara da cewa an tabbatar mata cewa mutane 416 na nan da rai, saɓanin wasu rahotannin da aka riƙa yaɗawa a baya.
Ƙungiyar ta bayyana kanta a matsayin muryar matasan Kudancin Borno, tana mai cewa za ta ci gaba da bin dukkan hanyoyin da suka dace, ciki har da sasanci da kira ga gwamnati domin ganin an sako waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya.
Sai dai BOSYA ta jaddada cewa ba ta goyon bayan ta’addanci ko garkuwa da mutane, amma tana ɗaukar wannan mataki ne domin ceton rayukan al’ummar yankin. Ta kuma buƙaci shugabanni ciki har da Bola Ahmed Tinubu, Kashim Shettima da Sanata Mohammed Ali Ndume su ɗauki matakin gaggawa.
Ƙungiyar ta kuma yi nuni da yadda aka taɓa samun nasarar sako mutane a jihohin Sokoto, da Zamfara, da Katsina da Kebbi ta hanyar shiga tsakani da wasu mutane kamar Ahmad Gumi, tana mai kira ga a nuna irin wannan himma a lamarin Ngoshe, tare da buƙatar haɗin kan ƙasa da ƙasa domin tabbatar da sakin dukkan waɗanda aka sace.
