Daga Mustapha Abdullahi
Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta yi gargadi ga lauyoyi da Alkalai da sauran ma’aikatan shari’a da su guji tsoma baki a harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa, yayin da ake tunkarar zaben 2027.
A wata sanarwa da shugaban NBA, Afam Osigwe, ya fitar a yau Juma’a, ya nuna damuwa kan wasu abubuwan da ke faruwa a fannin siyasa da shari’a, musamman yadda ake fassara da aiwatar da Dokar Zaɓe ta shekarar 2026.
Osigwe ya yi kashedin cewa irin wannan tsoma baki na iya zama barazana ga tsarin mulki, dimokuradiyya da kuma doka.
Ya kuma soki yadda ake yawaita shigar da ƙara kan rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyu, duk da cewa doka ta hana kotuna sauraron irin wadannan batutuwa.
Karanta:World Health Day: Bauchi Health Officials Promote Awareness, Digital Healthcare Among Student Nurses
Ya jaddada cewa dokar ta hana kotuna sauraron irin wadannan shari’o’i, har ma da bayar da umarnin wucin gadi a kansu.
Osigwe ya kuma tunatar da lauyoyi nauyin da ke kansu, yana mai cewa su “masu hidima ne ga adalci,” ba wakilan siyasa ba.
Ya gargadi cewa duk wani lauya da aka samu yana shigar da irin wadannan ƙara na iya fuskantar hukunci daga Kwamitin ladabtar da lauyoyi.
Haka kuma, NBA ta bukaci alkalai da su yi taka-tsantsan, su guji shiga harkokin siyasa da doka ta haramta, tare da kira ga Majalisar Shari’a ta Ƙasa (NJC) da ta hukunta duk wani alkalin da ya ƙarya wannan ka’ida.
Kungiyar ta kuma bukaci Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) da ta kasance ƴar-ba-ruwa-na a harkokin jam’iyyu domin kiyaye tsarin dimokuradiyya.
Recent:APC reshen jihar Kano ta yaba da ziyarar da shugaban jamiyyar na kasa ya kawo
