Daga Mustapha Abdullahi
An kashe Birgediya Janar Oseni Omoh Braimah, kwamandan Rundunar Task Force ta 29 ƙarƙashin Operation Hadin Kai, bayan wani mummunan hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a Benisheikh, Jihar Borno.
Karanta:An karrama Gwamna Dauda Lawal da lambar yabo bisa gina ayyukan raya jihar Zamfara
Rahotanni sun nuna cewa babban jami’in ya rasu ne yayin harin da aka kai kan sansanin sojoji, wanda hukumomi suka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin hare-haren da suka fi muni a baya-bayan nan a yankin Arewa maso Gabas.
Mutuwarsa ta zama babban rashi ga rundunar sojin Najeriya da ma ƙasa baki ɗaya, inda ake ci gaba da aika saƙonnin ta’aziyya domin girmama jarumtarsa, jagorancinsa, da kuma sadaukarwarsa wajen yaƙi da ta’addanci.
Recent:Wajibi dakarun Nijeriya su rika musayar bayanan sirri – Ministan Tsaro.
