Ministan wasannin ƙasar ta Iran, Ahmad Donyamali, ya ce ba za su buga kofin duniya ba sabida, Amurka ta kashe Jagoran addininsu, Ayatollah Ali Khamenei.
Ya kara da cewa, la’akari da yadda gurɓatacciyar gwamnatin Amurka ta kashe jagoranmu, babu wani hali da zai sa mu iya buga gasar kofin duniya.
Gasar cin kofin duniya ta bana dai, za ta gudana a ƙasashen Amurka, Canada da kuma Mexico.
